Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Amurka Tana Sanya Idanu Kan ‘Yan Boko Haram


Janar David Rodriguez, kwamandan rundunar sojojin Amurka dake kula da Afirka, AFRICOM
Janar David Rodriguez, kwamandan rundunar sojojin Amurka dake kula da Afirka, AFRICOM

Amma kuma jami’an gwamnatin Amurka su na daukar ayyukan kungiyar a Arewacin Najeriya a zaman batun cikin gida, wanda gwamnatin Najeriya ce ya fi dacewa ta takale shi.

Babban kwamandan Rundunar Sojojin Amurka a Afirka, Janar David Rodriguez, yace sojojin Amurka su na sanya idanu sosai a kan take-taken ‘yan Boko Haram na Arewacin Najeriya, a yayin da kungiyar take fadada huldarta da wasu kungiyoyin ta’addanci dake nahiyar Afirka.

Janar Rodriguez, wanda ya karbi ragamar shugabancin wannan runduna da ake kira AFRICOM a takaice, wadda kuma ta ke da hedkwata a Stuttgart dake kasar Jamus, yace daya daga cikin babban abinda suka bayar da muhimmanci gare shi, shi ne yaduwar kungiyoyin tsagera a Afirka. Yace musamman ma, sun sanya idanu a saboda damuwa da suke da ita ta musamman kan kungiyar Boko Haram a saboda a wani bangare, kungiyar tana ci gaba da fadada huldarta da kungiyoyin ta’addanci na yankin.

Ya ce, “mun damu da wannan domin irin wannan hulda tana fadada dama da fadada kwarewa ga irin wadannan kungiyoyi, kuma mun san Boko Haram kungiya ce mai son zub da jini sosai. Kungiya ce da ta ke yin illa ga yankin arewacin Najeriya, har ma da wasu sassan Nijar da Chadi…Za a bukaci yunkurin hadin kai daga wadannan kasashe, da kuma tsara shawara da dabaru masu kyau domin gwamnatin Najeriya ta samu ta shawo kan wannan matsalar.”

Sai dai jami’an gwamnatin Amurka su na daukar ayyukan na kungiyar Boko Haram a arewacin Najeriya a zaman wani batu na cikin gida, kuma su na ganin cewa abinda ya fi dacewa shi ne a kyale gwamnatin Najeriya ta takale shi.

Janar Rodrigudez yace rawar da rundunar sojojin Amurka ta ke takawa a nahiyar ita ce ta samar da horaswa da tallafi ga rundunonin sojan kasashen da suka bukaci taimakon. Ya ce sojojin Amurka, sun sanya idanu sosai a kan Kungiyar Boko Haram, yana mai cewa, “Dukkan abubuwan da suke gurgunta kasa, sune ya kamata mu sanya idanu a kai sosai, domin wadannan abubuwan ne zamu bayarda taimako wajen shawo kansu, watau tallafawa kasashen na Afirka ta yadda su da kansu zasu iya maganin wannan lamarin. Wannan shi yasa muke aikin karfafa yadda kasashe kawayenmu na Afirka zasu iya tabbatar da tsaronsu.”

Sansani kwaya daya tak da Amurka take da shi a nahiyar Afirka shi ne wanda yake Djibouti, kuma ta ce ba ta da niyyar sake gina wani. Amma kuma rahotannin fadada ayyukan sojan Amurka, ciki har da ayyukan leken asiri da jiragen saman nan da ake kira “Drone” wadanda ke shawagi babu kowa cikinsu a Nijar da kuma Mali, sun kara janyo hasashen cewa Amurka tana shirin kara taka rawa a nahiyar Afirka.
XS
SM
MD
LG