Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sanda Ta Samo Hanyar Yaki da Cin Hanci


'Yansandan Najeriya suke sintiri.
'Yansandan Najeriya suke sintiri.

A wani kokari na wanke kanta daga irin halayen da aka san 'yan sandan Najeriya da shi, yanzu rundunar tace ta samo sabuwar hanyar yaki da cin hanci da rashawa.

Rundunar 'yan sandan Najeriya tace ta samu wasu sabbin dabarun ganin jami'anta sun kau da kansu daga karban na goro daga jama'a wadanda ba zasu bayyana a bainar jama'a ba.

Rundunar tace duk wanda ta samu yana tursasawa jama'a to idan ya shiga hannu ya kwana da sanin cewa ya debo ruwan dafa kansa ne. Mataimakin sifeton 'yan sanda Mamman Ibrahim Tsafe shi ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.

Duk da yake suna neman karin albashi amma sifeto janaral nasu na iya bakin kokarinsa domin samarda wasu abubuwan jin dadi da ka karawa 'yan sandan kwarin gwiwa. Yayin da rundunar ke kokarin yin abubuwan da ka iya sa su ji dadin ayyukansu amma kuma duk wanda ya taka doka ya gama yawo. Babu inda za shi.

An roki jama'a su saki jiki su dinga ba manyan jami'an 'yan sanda bayanai akan wadanda suke aikata ayyukan asha ko da ma jami'an 'yan sanda ne.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG