Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Ekiti Zata Tabbatar an Gudanar Da Zaben Gwamnan Jihar Cikin Lumana


M.D Abubakar, Sefeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya
M.D Abubakar, Sefeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya

Rundunar 'yansandan jihar Ekiti tace a shirye take ta tabbatar an gudanar da zaben gwamnan jihar wanda za'a yi ranar 21 ga wannan watan cikin lumana da kwanciyar hankali

A jihar Ekiti rundunar 'yansandan jihar tace ta shirya tsaf domin ta tabbatar an gudanar da zaben gwamnan jihar ranar ashirin da daya na wannan watan ba tare da tashin hankali ko hatsaniya ba.

Kakakin rundunar Mr. Victor Babayemi shi ya shaidawa manema labarai a birnin Ado Ekiti fadar gwamnatin jihar. Yace duka jami'an tsaro zasu yi aiki tare domin su tabbatar da doka da oda a lokacin zaben gwamnan jihar kana za'a sanya 'yansanda uku a kowace rumfar zabe. Ban da haka za'a baza jami'an tsaro shida ko bakwai a kowace runfar zaben.

Babayemi yace wani lokaci 'yan siyasa suna bada dariya saboda wasunsu suna da halaye da basu dace da matsayinsu ba. Yace za'a karo jami'an 'yansanda dubu biyu daga jihohi dake makwaftaka da jihar domin dakile duk wata tashin tashina a lokaci da kuma bayan zaben. Kakakin ya bayar da lambobin wayar tarho da za'a kira idan akwai matsala a koina.

Rundunar zata kuma yi anfani da jiragen sama biyu da karnukan 'yansanda da dawakin 'yansanda duk a kokarin tabbatar da doka da oda lokacin zaben da kuma bayan an kammalashi.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG