Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Sama Da Tabo da Laka Su na Rage Ma Sojojin Kenya Hamzari...


Sojojin Kenya a kusa da garin Liboi a bakin iyakarta da kasar Somaliya, ranar 15 Oktoba 2011
Sojojin Kenya a kusa da garin Liboi a bakin iyakarta da kasar Somaliya, ranar 15 Oktoba 2011

A yayin da suka kutsa cikin yankuna akalla biyu na Somaliya makwabciyarsu domin farauto ‘ya’yan kungiyar kishin Islama ta al-Shabab.

Sojojin kasar Kenya su na fuskantar matsalolin ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma laka da tabo kan hanyoyi, a yayin da suka kutsa cikin yankuna akalla biyu na Somaliya makwabciyarsu domin farauto ‘ya’yan kungiyar kishin Islama ta al-Shabab.

An ce a yanzu haka sojojin Kenya su na kusa da garin Afmadow dake hannun al-Shabab a yankin Jubba na Somaliya, inda aka ce mazauna su na ta gudu domin tsoron kada a rutsa da su a fadan da ake ji za a gwabza.

Jami’ai da shaidu sun fadawa Muryar Amurka jiya talata cewa sojojin Kenya, tare da jiragen yakinsu na helkwafta, sun shige ta garin El-Waq dake bakin iyaka suka shiga cikin yankin Gedo na Somaliya.

Jiya talata a babban birnin na Somaliya, watau Mogadishu, jami’an gwamnatin Kenya da na Somaliya sun yi alkawarin daukar matakan rigakafin hare-hare a kan kungiyoyi masu makamai dake barazana ga kasashen biyu. Da alamun yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma ta takaita matakan sojan da kasar Kenya zata iya dauka a cikin yankin Jubba ta kasa kawai.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG