Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Kundin Tsarin Mulkin Kenya


Mutanen Kenya na shirin jefa kuri’ar amincewa da sabon kundin tsarin mulkin da ake fatar zai taimaka wajen warware matsalolin banbancin kabilanci da na akidar siyasar da aka dade ana fama da su.

A cikin wannan makon ne mutanen Kenya zasu jefa kuri’ar amincewa ko akasin haka da sabon kundin tsarin mulkin da aka fito da shi da fatar zai taimaka a warware matsalolin banbancin kabilanci da na akidar siyasar da aka yi shekaru ana fama da su. Ra’ayoyin jama’a da aka ji zuwa yanzu dai suna nuna goyuon bayan al’umma ga wannan kundin wanda kuma har ila yau yake da goyon bayan shi kansa shugaban kasar ta Kenya Mwai Kibaki da mataimakinsa Raila Odinga.

Kundin da ake anfani da shi a yanzu ana zargin ya baiwa shugaban kasa iko mai yawan gasken dake bashi damar yin abinda ya ga dama da ma’aikatun gwamnati da dukiyar jama’a, wadanda aka ce yafi bayarwa ga ‘yan kabilarshi. Amma sabon kundin ya rage yawan ikon shugaban, ya karawa yankunan kananan hukumomi tasiri, ya kuma kayyade yawan ministoci zuwa 22. Haka kuma kundin ya kirkiro majalisar dokoki ta biyu, ya kuma kawarda mukamin frayim-minista.

XS
SM
MD
LG