Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP Zai Iya Hada Kawunan 'Yan Jam'iyyar?


Wasu gwamnonin da suka fice daga PDP
Wasu gwamnonin da suka fice daga PDP

Duk da zaben sabon shgaba da jam'iyyar ta yi har yanzu ana tambaya ko zai iya hada kawunan 'yan jam'iyyar ya kuma dawo da wadanda suka fice?

Bayan an zabeshi Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu ya bayyana irin yadda suka yi hulda da tsohon shugaban da ya sauka.

Abun da ya faru tamkar fadi ne da Alhaji Bamanga Tukur ya yiwa sabon shugaban jam'iyyar. Da yake jawabi bayan zabensa ya ce ya tuna cewa duk lokacin da ya duka ya gayar da Alhaji Bamanga Tukur sai ya ce masa kada ka yi garaje. Zan mika maka ragamar shugabancin jam'iyyar nan.

Manyan 'yan PDP suna ganin Alhaji Mu'azu zai iya dawo da wadanda suka fice daga jam'iyyar musamman tun da ya karfafa fitar da gwani kafin tsayar da dan takara. Hakan ya nuna matukar shugaba Jonathan zai tsaya takarar shugaban kasa to dole sai ya fuskanci hamayya. Haka ma zata faru da masu takarar gwamnoni da sauran mukamai.

Onarebul Inuwa Dauda kakakin majalisar dokokin jihar Gombe kuma shugaban kakakin dokoki na majalisun Najeriya ya ce zai bada gudummawa wurin tattaro duk 'ya'yan jam'iyyar su zo su hada kai a cigaba da ba jam'iyyar goyon baya domin su cigaba da samun nasara da kuma dorewar tattalin arzikin kasar.

Kafin zaben sabon shugaban shugaba Jonathan ya ce lallai a toya komi gaban 'yan jarida, kada a yi rufa rufa. To yanzu tambaya ita ce wadanda suka fice zasu dawo ne tun da an samu sabon shugaba wanda ya yi alkawarin shimfida adalci? Alhaji Ado Doguwa daya daga cikin wadanda suka canza sheka zuwa APC ya ce canza Bamanga Tukur daya ne daga cikin abubuwa da yawa da suka bukaci a gyara. Sun bada dama a gyara amma yanzu damar da suka bayar ta wuce. Ya ce jam'iyyar PDP da ya sani can baya ta mutu. Ya jawo hankalin Mu'azu ya duba tarihin PDP. Babu shugaban da ya fara lafiya ya kuma kare lafiya tun daga lokacin da aka kafata. Kujerarar da ya dauka yanzu ba abun a yi masa murna ba ne abun a jajanta masa ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG