Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Didier Drogba Yace Sai 'Yan Sa'o'i Kafin Wasa Zai Yanke Shawara Kan Ko Zai Buga


Kyaftin din na 'yan wasan Ivory Coast yace talata ana dab da wasa zai ga ko kariyar da yayi a hannu zata kyale shi ya buga ma kasarsa a karawar farko da zata yi da Portugal

Kyaftin na 'yan wasan kwallon kafar kasar Ivory Coast, Didier Drogba, yace sai kasarsa tana dab da bugawa da Portugal a wasansu na farko wajen gasar Cin Kofin Duniya, zai yanke shawara a kan ko zai buga.

Dan wasan na kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea a Ingila mai shekaru 32 da haihuwa, ya karya wani kashi a hannunsa na dama a lokacin wasan tayar da tsimi na karshe da kasarsa ta yi da Japan ranar 4 ga watan Yuni a Switzerland. Yau litinin kwana biyu ke nan a jere Drogba yana halartar motsa jiki na kungiyar Ivory Coast a bayan da aka yi masa tiyata a hannun.

A bara, Drogba shi ne dan wasan da ya fi jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig-lig na kasar Ingila.

Mai koyar da 'yan wasan Ivory Coast, Sven-Goran Eriksson, yace Drogba zai yanke shawara sa'o'i biyu kafin gwabzawar da kasar zata yi da Portugal talata a garin Port Elizabeth a Afirka ta Kudu.

Har ila yau, sai Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta duba ta kunma amince da Filasta da aka daure hannun Drogba da ita kafin a kyale shi ya buga. Hukumar zata nazarci filastar ce domin tabbatar da cewa ba zata zamo hatsari ga sauran 'yan wasa ba.

An bayyana wannan rukuni na 7 ko "G" inda kasar Ivory Coast take a zamanin rukunin mutuwa a gasar cin kofin Kwallon Duniya a bana a saboda karfin kasashen dake wannan rukuni. A bayan ita Ivory Coast akwai kasashen Brazil, da Portugal da kuma Koriya ta Arewa.

XS
SM
MD
LG