Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon zaben shugaban kasar Nigeria ya nuna shugaba Jonathan ne ke samun nasara


Nan masu zanga-zanga ne dauke da sanduna da barandamai ke zanga-zanga a birnin Kano Arewacin Nigeria, inda ake tafka rikici tsakanin masu zanga-zanga da jami'an soja ran litinin 18 ga watan Afrilun shekarar 2011,bayan fara bayyana sakamakon zaben dake n
Nan masu zanga-zanga ne dauke da sanduna da barandamai ke zanga-zanga a birnin Kano Arewacin Nigeria, inda ake tafka rikici tsakanin masu zanga-zanga da jami'an soja ran litinin 18 ga watan Afrilun shekarar 2011,bayan fara bayyana sakamakon zaben dake n

Nasarar da shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya samu a zaben shugaban kasa, hakan ya haifar da rikici da tashe-tashen hankula. Bayan an bayyana sakamakon zaben daga jihohin Nigeria 31 daga cikin talatin da shida yau litinin, hakan ya nuna Jonathan na sahun gaban babban abokin takararsa janar Muhammadu Buhari da mafi yawan kuri’un da aka kada.

Da jin labarin cewa shugaba Goodluck Jonathan ne ya sami nasara, sai tarzoma ta barke a a mafi yawan jihohin Arewacin Nigeria inda Muhammadu Buhari yafi samun kuri’u da goyon baya. Buhari dai Musulmi ne kuma tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojan Nigeria. Rahotannin da ‘yan sandan Nigeruia ke bayarwa na cewa masu zanga-zanga kin amincewa da sakamakon zaben na Nigeria sun bazama kan titunan birnin Kaduna inda aka bada labarin tashin bom a daren Asabar a wani Otel harma mutane takwas suka jikkata. Kazalika ‘yan sanda sun bada rahoton tashin hankali da kone-kone a biranen Kano da Zaria.

Duk da haka jami’an dake nazartar yadda aka gudanar da zaben sun ce anyi zaben cikin ‘yanci da walwala im banda coge-da dan magudin da aka yi jifa-jifa nan da can. A halin da ake ciki, jami’an tsaron Nigeria sun shiga loko-loko a wuraren da aka bada rahoton tashin hankali domin kokarta maido da zaman lafiya a Nigeria. A yadda al’amuran ke tafiya a yanzu haka dai idan har hukumar zaben Nigeria ta ayyana Mr. Goodluck Jonathan shine ya sami nasarar zama sabon shugaban kasa, ba lallai bane aje zagaye na biyu domin fidda gwani ba, domin ya riga ya sami sama da rabin kuri’un da zasu hana sake kaiwa ga zagaye na biyu a zaben.

XS
SM
MD
LG