Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Zaben Super Tuesday Na Amurka


Hillary Clinton na jam’iyar Democrat da Donald Trump na jam’iyar Republican sun samu nasarar karfafa samun jam’iyun su su tsayar da su yan takarar shugaba, a yayinda suka lashe muhimmancin jihohi a zaben gandu na fidda yan takara da aka yi jiya Talata da ake cewa Super Tuesday, a zamar ranar mafi muhimmanci a zaben na tsayar da dan takara.

Kafofin yada labaru sun yi has ashen cewa tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton ta doke abokin hamiyarta Bernie Sanders a jihohi shidda na kudancin Amirka da suka hada da Tennessee da Alabama da Georgia da Arkansas da Virginia da kuma Texas.

Bernie Sanders kuma ya zama zakara a jihar sa ta Vermont da Oklahoma.

A bangaren jam’iyar Republican kuma Donald Trump ya lashe jihohin Georgia da Alabama da Tennessee da Virginia da kuma Masachusetts. Senator Ted Cruz yayi nasara a jiharsa ta Texas da kuma Oklahoma.

Senator Marco Rubio daga mazabar jihar Florida, shi kam ko jiha daya bai ci ba, ake ganin cewa kila ko kuri’a day aba zai samu ba.

Wannan sakamako bai bada mamaki ba,domin kididdigar jin ra’ayi sun nuna cewa Hillary Clinton da Donald Trump sune zasu yi rawar gani.

XS
SM
MD
LG