Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Tsaron Amurka Zai Kai Ziyara Masar


Jim Mattis
Jim Mattis

A yau Alhamis ne sakataren tsaron Amurka Jim Mattis zai kai ziyara a kasar Misra, a ci gaba da tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin Washington da Alkahira a farkon kwanaki 100 na gwamnatin Trump kan mulki.

Ana sa ran Mattis, zai gana da ministan tsaron misra Sedki Sobhy da shugaban ma’aikatar sojin kasar Lt Genera Mahmoud Hegazy da ma shugaba Abdel Fattah el-Sissi, wanda ya ziyarci fadar White House a farkon wannan wata wanda shine na shugaban Misran a farko da ya yi wannan ziyara tun bayan da shugaba Barack Obama ya karbi bakwancin Hosni Mubarak a shekarar 2009.

Boren siyasa da ya yi sanadiyar hambarar da Hosni Mubarak daga kan mulki, da kuma kwashe shekaru ana hargitsi shine ya kawo tsohon shugaban soji janar Sissi bisa karagar mulki.


Wani mai fashin baki kan Gabas ta Tsakiya James Gelvin, kuma shehun malami a jami’ar California a birnin Los Angeles, ya fadawa Muryar Amurka cewar galibin tsare-tsaren gwamnatin Trump yana nuna adawa da shugaba Obama.

Anasa rana Mattis zai bawa Misra da take fama da kalubalolin siyasa da na kudi da tsaro kwarin gwiwa da ta yi tsayin daka wurin yaki da ta’addanci wanda ke zama barazana ga sashen Larabawan Sinawa da ma wasu birane, kamar yadda ya bayyana a wani hari da mayakan ISIS suka kai inda suka hallaka mutane a wasu Majami’u.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG