Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Ndume Yace Meye Na Kafa Kwamiti Ga Majalisa


Ginin Majalisar Dokokin Najeriya a Abuja
Ginin Majalisar Dokokin Najeriya a Abuja

Sanata Ali Mohammed Ndume yace mutane 13 ba su isa su iya sanin illahirin matsalolin da ke damun Najeriya ba

Dan majalisar dattawan Najeriya mai wakilitar kudancin jahar Borno Sanata Mohammed Ali Ndume ya ce kwamitin da shugaban kasa Goodluck Jonathan Ebele ya kafa don ya bashi shawarwari akan shirya babban taron tattauna matsalolin da su ka addabi kasar tamkar kishiya ya yiwa 'yan majalisa ba tare da biyan sadaki ba.

Dan majalisar yayi wannan furuci ne a yayin tattaunawar shi da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a birnin Maiduguri, Haruna Dauda Biu. Sanata Ali Mohammed Ndume ya ci gaba da cewa ta hanyar gyara kundin tsarin mulkin kasa ne kawai za a iya tabo duka irin wadannan matsaloli amma ba kamar yadda shugaban kasar yayi ba ta hanyar zabo mutane goma sha uku kawai daga cikin jahohin kasar talatin da shida, har da Abuja babban birnin tarayya.

Sanatan ya ce mutanen nan goma sha uku da shugban ya zabo ba za su iya sanin illahirin matsalolin da kasar Najeriya ke fama da su ba. Sannan ya ci gaba yin bayani kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG