Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sankarar Makogwaro Ba Za ta Hana Shugabar Argentina Aiki Ba


Shugabar kasar Argentina, Cristina Fernandez de Kirchner, wadda ke shirin fara jiyyar cutar sankarar makogwaro a makon gobe
Shugabar kasar Argentina, Cristina Fernandez de Kirchner, wadda ke shirin fara jiyyar cutar sankarar makogwaro a makon gobe

Shugabar kasar Argentina ta yi kudirin ci gaba da aiki cikin jiyyar cutar sankara

Shugabar kasar Argentina ta yi alkawarin kara sadaukar da kai ta yiwa kasar ta aiki a lokacin da za ta yi jiyyar cutar sankarar makogwaro, bayan an yi ma ta aikin fida.

A fitar ta, ta farko bainar jama'a jiya a jiya Laraba tun bayan da aka yi sanarwar kamuwar ta da cutar, shugaba Cristina Fernandez de Kirchner ta na cikin kuzari da walwala. Ta ce za ta maida hankali sosai kan mataimakin ta wanda zai tafiyar da harakokin mulkin kasar lokacin da za ta yi hutun jiyya na kwanaki 20, har ma cikin raha, ta yi zolayar cewa ya kamata mataimakin na ta , ya shiga hankalin shi.

Ranar Talatar da ta gabata wani kakakin gwamnatin kasar ya yi sanarwar cewa a makon jiya likitoci sun gano cewa shugabar ta na da sankarar makogwaro. Kakakin ya ce cutar sankarar ba ta nuna alamun bazuwa da gama jiki ba, kuma idan aka yi jiyyar ta, ta na warkewa da kyau. A makon gobe za a yiwa shugabar kasar aikin fida a babban asibitin Austral, a Buenos Aires babban birnin kasar na Argentina.

A shekarar da ta gabata, shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya yi jiyyar cutar sankarar mara a kasar Cuba, shi ma tsohon shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya fara jiyyar cutar sankarar makwallato. Haka ita ma shugabar kasar Brazil mai ci, Dilma Rousseff, ta yi jiyyar cutar sankara jim kadan kafin ta kama aiki a cikin watan janairun da ya gabata.

Shugabar kasar Brazil ta yanzu, Dilma Rousseff, tare da tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, wanda ya mika ma ta mulki, kuma dukan su biyu sun yi fama da cutar sankara
Shugabar kasar Brazil ta yanzu, Dilma Rousseff, tare da tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, wanda ya mika ma ta mulki, kuma dukan su biyu sun yi fama da cutar sankara

A cikin wani jawabin da ya yi ta talbijin ja iya Laraba, Mr.Chavez mai fitowa fili karara ya na sukan lamirin Amurka akai-akai, ya ce watakila ma Amurka ce ta ke bin shugabannin kasashen kudancin nahiyar Amurka ta na hada su da cutar sankara cikin wani shirin ta na mugunta da nufaka.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG