Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudi Arabiya Ta Gargadi Turai Cewa Al-Qa'ida Tana Kulla Kai Hari


Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Brice Hortefeux, yana ganawa da jami'an tsaro a hasumiyar nan ta Eiffel Tower dake Paris, alhamis, 16 Satumba, 2010.
Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Brice Hortefeux, yana ganawa da jami'an tsaro a hasumiyar nan ta Eiffel Tower dake Paris, alhamis, 16 Satumba, 2010.

Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Brice Hortefeux, yace yace wannan barazana ta zahiri ce, kuma gwamnatin Faransai ta daura damara.

Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Brice Hortefeux, yace kasar Sa’udiyya ta yi gargadin cewa kasashen Turai, musamman ma kasar Faransa, su na fuskantar wata barazanar ta’addanci daga kungiyar al-Qa’ida. Hortefeux ya fadawa gidajen rediyo da telebijin na Faransa a jiya lahadi cewa a cikin ‘yan kwanakin nan hukumomin leken asiri na kasashen Turai suka samu wannan gargadin daga hukumomin Sa’udiyya.

Yace wannan barazana ta zahiri ce, kuma gwamnati ta daura damara.

A farkon wannan wata Amurka da Britaniya da kuma Japan suka gargadi ‘yan kasashensu game da yiwuwar fuskantar hare-haren ta’addanci a Turai a bayan da jami’an leken asiri na kasashen yammaci suka bankado wata makarkashiyar da tsagera masu alaka da kungiyar al-Qa’ida a Pakistan suke kullawa ta kai hare-hare a manyan biranen kasashen Britaniya da Faransa da kuma Jamus.

Jami’an suka ce hare-haren su na iya yin kama da na 2008 da aka kai a Mumbai a kasar Indiya, inda aka kashe mutane 166 aka raunata wasu da da

XS
SM
MD
LG