Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauyin Manyan Shugabannin Sojan Najeriya Na Nufin Sauyi A Yadda Ake Yakar Boko Haram


Wani tankin yaki na sojojin Najeriya lokacin faretin cikar shekaru 150 da kafa rundunar a Abuja.
Wani tankin yaki na sojojin Najeriya lokacin faretin cikar shekaru 150 da kafa rundunar a Abuja.

Kwararru sun ce gazawa a yaki da Boko Haram it ace ta sa shugaba Goodluck Jonathan ya saukar da dukkan manyan hafsoshin kasar a makon da ya shige

A bayan da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kori manyan hafsoshi masu jagorancin rassan rundunar sojan kasar a makon da ya shige, masu fashin baki da yawa sun ce wannan alama ce dake nuna cewa manyan hafsoshin sun kasa shawo kan Boko haram a arewacin kasar. Wasu daga cikinsu sun ce da alamun shugaba Jonathan yana shirin bullo da sabuwar dabara ce ta takalar matsalar tsaron da kasar ke fuskanta kafin zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Yau watanni 8 ke nan sojoji sun a mamaye da wasu jihohi uku a yankin arewa maso gabashin Najeriya, amma duk da haka, ‘yan bindiga sun a ci gaba da kai hare-hare.

A lokacin da shugaba Jonathan yake bayyana sabbin shugabannin rundunonin kasa, da na ruwa da na sama da kuma babban hafsan tsaro na kasar a ranar alhamis na makon jiya, bai bayyana dalilinsa na yin hakan ba. Amma kuma wani mai fashin bakin siyasa da ake kira Fabian Ihekweme, yace da alamun shugaban yana gwada wata sabuwar dabara ce ta takalar wannan matsalar tsaron.

Yace, “idan ba a manta ba, kwanaki kalilan da suka shige ne aka kafa wata sabuwar rundunar zaratan sojoji ta yaki da ta’addanci a cikin rundunar sojan Najeriya. Don haka ina jin wannan wani bangare ne na sabuwar dabarar da shugaban yake tsarawa na takalar Boko Haram.”

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce an kasha mutane 40, wasu 50 suka ji rauni a lokacin da bam ya tashi cikin mota a talatar makon jiya a garin Maiduguri, cibiyar wannan kungiya ta Boko Haram.

A watan da ya shige, ‘yan bindiga sun kai hari cikin dare a garin na Maiduguri, suka lalata wani sansanin soja, da caji ofis na ‘yan sanda, da gidan mai, da kuma motoci masu yawa. Har ila yau sun kai farmaki a kan wani sansanin mayakan sama.

Kungiyar Boko Haram ta kasha dubban mutane a cikin shekaru 4 da ta yi tana tayar da kayar baya, kuma ci gaban wannan tashin hankalin ya raunana farin jinin shugaba Jonathan yayin da babban zabe na 2015 yake kara matsowa.

Manyan jami’ai da dama, ciki har da gwamnoni biyar da ‘yan majalisa masu yawa da wasunsu sun fice daga cikin jam’iyyar PDP mai mulkin lasar. Ala tilas Bamanga Tukur ya sauka daga kan kujerar shugabancin jam’iyyar ta PDP, aka kuma nada tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Ahmadu Adamu Mu’azu, a zaman shugabanta na riko bisa fatar sake zawarcin gwamnoni da ‘ya’yan jam’iyyar da suka fice.

Sai dai darektan wata cibiyar nazarin manufofi da shari’a mai zaman kanta da ake kira “Policy and Legal Advocacy Centre” a Abuja, Clement Nwanko, yace zai yi wuya wadanda suka gudu daga jam’iyyar su komo, domin ba wai Bamanga Tukur ne da ma ainihin matsalarsu ba, kuma ba wai domin dalilan tsaro ne suka bijire din ba.

Yace wasu shugabannin sun a ganin cewa idan har Jonathan ya sake tsayawa takarar shugaban kasa, to tamkar ya karya alkawarin da suka yi su ya sunsu ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP ne cewa za a rika juya ragamar takarar shugabancin kasar, a rika yin karba-karba a tsakanin arewaci da kudanci.

Shugaba Jonathan, wanda ya fito daga kudancin kasar, ya sha yin alkawarin cewa zai ga bayan kungiyar Boko Haram. A karkashin dokar-ta-bacin da ya kafa, sojoji sun kame manyan alkaryu, suka kasha ko suka kama daruruwan ‘yan Boko Haram. Amma duk da haka an ci gaba da kai hare-hare a kananan garuruwa da kauyuka na karkarar yankin.

Hare-haren da aka kai kwanakin baya a Maiduguri, sune na farko a cikin babban birnin na Jihar Borno tun lokacin da aka kafa dokar-ta-baci a cikin watan Mayun bara.
XS
SM
MD
LG