Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Ta Kafa Kotun Ta Musamman Domin Hukunta Hissen Habre.


Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall
Wakilan majalisar dokokin Senegal sun zartas da wata doka da zata kafa wata kotu ta musamman wacce zata hukunta tsohon shugaban kasar Cadi Hissen Habre kan zargin laifuffukan cin zarafin BilAdama.

Majalisar dokokin kasar ta amince da yarjejeniya da kasar ta kulla da tarayyar Afirka na kafa kotun wacce aka lakabawa sunan “azure na musamman”.

Kungiyoyin kare hakkin BilAdama sun sha yin kira cikin shekaru masu yawa d a suka wuce ga Senegal ta hukunta Habre, wanda aka yiwa daurin talala a birnin Dakar tun 1990.

An gabatar da tuhuma akansa tun a shekara ta 2000, amma tsohuwar gwam,natin kasar ta gaza yin kome akai.

Habre ya shugabanci Cadi daga 1982- 1990, kamin Idris Deby yayi masa juyin mulki.

kwamitin bin kadun gano gaskiya a Cadi, ta bada rahoto a 1992 cewa, Habre yana da hanu a kisan fiye da mutane dubu 40 kan dalilan siyasa, ganawa mutane aku ba, da kuma keta haddin BilAdama.
XS
SM
MD
LG