Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shaikh Dahiru Bauchi Ya Yaba da Salon Mulkin Buhari


SHAIKH DAHIRU BAUCHI
SHAIKH DAHIRU BAUCHI

Mai wa'azin addinin musulunci Shaik Usman Bauchi yace a kwanaki dari na farkon mulkin Buhari an samu takawa kungiyar Boko Haram birki

Shaikh Dahiru Usman Bauchi yace an kuma samu inganta rayuwar 'yan kasa tare da yaki da cin hanci da rashawa.

Cikin kwanaki dari Allah ya nunawa al'ummar Najeriya alamun cin nasara na zaman lafiya. Kafin wannan lokacin yawancin yankunan jihohin Yobe, Borno da Adamawa suna hannun 'yan Boko Haram ne amma yanzu an kwatosu.

'Yan Boko Haram sun yadu sosai saboda a rana daya sun kashe mutane fiye da dubu biyu a Baga suka cigaba da sarafa bom kusa da Ashaka kana suna kai hare hare Nafada da Bajoga da Gombe da Azare. Har cikin Masallacin Jumma'a na Kano sun kai hari. Amma cikin kwanaki dari da Buhari ya kama mulki Allah ya kawar dasu an zauna lafiya.

Yanzu 'yan Boko Haram basu da karfin kai hari saidai su ne ake kaiwa hari yanzu. Saboda nasarar da Allah ya bayar suke gode mashi. Allah kuma ya bada lafiya da zaman lafiya d kwanciyar hankali.

Shaik Dahiru Bauchi bayan ya yi addu'a sai yace dalilin tara taron malamai ke nan domin a yiwa Allah godiya ta musamman.Ya godewa malaman da suka kasance a wurin addu'an tare da malaman da suka zauna garuruwansu ko kauyukansu amma suka yi addu'a.

Da ya amsa tambaya akan salon mulkin Buhari Shaik Bauchi yace shugaban na yaki da cin hanci da rashawa kuma ana yi masa addu'a Allah ya bashi nasara ya kuma ba kasar zaman lafiya ta kowace hanya. Ya ce Allah ya sa a maido da kudaden da aka kwashe domin an wawuresu an kaisu wasu wurare kafin ya kama mulki.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG