Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shayar da jarirai da nonon uwa yana kara masu basira


Wata mai jego da jaririyarta a asibiti
Wata mai jego da jaririyarta a asibiti

Wani bincike da aka gudanar a baya bayan nan na nuni da cewa yaran da aka shayar da nonon uwa sun fi basira

Wani bincike da aka gudanar a baya bayan nan tsakanin sama da jarirai dubu goma sha bakwai daga haihuwa har zuwa shekara shida da rabi, na nuni da cewa, yaran da aka shayar da nonon uwa zalla a watannin farko na haihuwa sun fi kwakwalwa da fahimta da wuri da kuma basira.

Binciken ya nuna cewa, jarirai da nauyinsu ya gaza ainihin yadda ya kamata nauyin jariri ya kasance a lokacin haihuwa, aka kuma fara basu nonon uwa da zarar aka haife su, suna kara nauyi su kuma yi girma nan da nan fiye da wadanda ba a shayar da nonon uwa ba.

Haka kuma binciken ya nuna cewa, jariran da aka shayar da nonon uwa basu rika yawan rashin lafiya har ya kai ga kwantar da su a asibiti ba. Bisa ga binciken kungiyar likitocin kananan yara ta Amurka, yana yiwuwa shayar da nonon uwa ya taimaka wajen hana yaro mummunar kiba. Suka kuma bada shawarar shayar da jarirai da nonon uwa domin kare su daga yin kazamar kiba. Jariran da aka shayar da nonon uwa zalla sun fi samun wannan amfanin, haka kuma koshin lafiyar yaro lokacin da yake gima ya danganta ga tsawon lokacin da aka dauka ana shayar da shi da nonon uwa.

Kwararru suna kyautata zaton cewa, shayar da jariri da nonon uwa yana shafar kibar yaro domin dalilan da dama da suka hada da cewa, jariran da aka shayar da nonon uwa, sun fi tsayawa su ci abinci su koshi, abinda ke taimakawa wajen cin abincin da ya kamata a lokacin da ya kamata kuma bayan sun yi girma.

Aika Sharhinka

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG