Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ko Gwamnatin Amurka Zata Baiwa Omar Al Bashir Visa?


Shugaban kasar Sundan Omar al-Bashir
Shugaban kasar Sundan Omar al-Bashir

Gwamnatin Sudan tana sa ran shugaba Barack Obama zai baiwa shugaba Omar Al Bashir takardar iznin shiga kasa ko kuma visa, domin ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York na wannan shekara.

Ministan yada labaran Sudan Ahmed Bilal ya ce babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki- moon ya mika goron gayyata ga shugaba Al Bashir domin ya halarci taron, wanda za a yi a watan Satumba.

Ya kuma ce hakkin ne da ya rataya a wuyan Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mai karbar bakuncin taron, ta baiwa Al Bashir visa.

Minista Bilal, ya ce a baya, Al Bashir ya nemi Visar amma aka hana shi, sai dai lura da cewa ya samu goron gayyata daga Majalisar Dinkin Duniya, bai kamata Amurka wacce ita ce mai masaukin baki, ta hana shi haraltar taron ba.

A makon da ya gabata, shugaba Al Bashir ya halarci taron rantsar da shugaba Yuweri Musuveni na Uganda a birnin Kampala, inda yayin jawabinsa, Museveni ya kwatanta kotun hukunta manyan laifuka ta ICC a matsayin taron mutane marasa amfani, lamarin da ya sa wakilan Amurka suka tashi suka fice daga taron.

Ita dai kotun ta ICC na neman Al Bashir ruwa a jallo, bayan da ta same shi da aikata laifukan yaki.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG