Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Shugaban Najeriya Nada Ikon Kara Wa'adin Dokar Ta Baci


Shugaba Jonathan
Shugaba Jonathan

A wata fira da shugaban Najeriya shugaba Jonathan yayi a karshen mako yace yana duba yiwuwar kara wa'adin dokara ta baci a jihohin Adamawa da Borno da Yobe. Shin shugaban nada ikon yin hakan.

A karshen makon da ya wuce shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace yana sake duba yiwuwar kara wa'adin dokar ta baci a jihohin nan uku wato Adamawa, Borno da Yobe.

To amma masana harkokin tsaro suna ganin yin hakan ba zai haifar da da mai ido ba idan aka yi la'akari da abubuwan dake faruwa yanzu.

Kungiyar dattawan arewa ta mayarda martani akan wannan sabon yunkuri na shugaban kasar.Tace sake kakaba dokar ta baci ba zai kawar da komi ba. Barrister Solomon Dalung na kungiyar dattawan yace a karkashin dokar Najeriya shugaban kasa bashi da ikon sake kakabawa jihohin dokar ta baci karo na uku. Yace amma a Najeriya komi na iya faruwa.

Solomon Dalung yace kafin a kafa dokar ta baci an riga an girke sojoji a wuraren amma duk da haka ba'a samu biyan bukata ba. Wannan ya isa ya nunawa gwamnati cewa kafa dokar ta baci karo na uku ba zai biya bukata ba. Maimakon haka ma za'a kara samun tabarbarewar tsaro ne. To amma yada majalisar kasar take komenene shugaba yake so zai samu muddin ya biyasu. Yanzu ma ana ganin matarsa ma yau ta baiwa kanta ikon kamawa da kulle mutum.

Solomon Dalung ya cigaba da cewa babu wanda zai san arewa fiye da dan arewa. Yace za'a kawo soja sai a kawo mutum daga kudu wanda bai san komi ba akan arewa wai ya zo ya aiwatar da tsaro. Yace sun riga sun ba shugaban kasa shawarwari kuma kamata yayi yayi aiki da su. Ba za'a iya tabbatar da tsaro a kowane wuri ba sai an samu hadin kan dattawa da al'ummar wurin, kamar su sarakuna da shugabannin matasa da na mata da dai sauransu.

Wani tsohon jami'in tsaro a kasar Manjo Yahaya Shinko mai murabus yace idan gwamnati da gaske ta keyi akan yaki da ta'adanci to dole sai ta sauya salo da yin anfani da lalama da kuma sasantawa. To amma wani malami yace ya san hanyar sasantawa da 'yan Boko Haram. Yace ya sansu domin yana yi masu gargadi kuma suna jinshi. Yace hanyar da za'a bi yace zai shiryawa shugaban kasa da kansa yadda zai yi kuma zasu yadda.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG