Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Wace Kasa ce Ta Fi Kwarewa Wajen Dafa Shinkafa Dafaduka


Jollof
Jollof

Gaddama ta taso ne akan wace kasa ce cikin kasashen Ghana da Najeriya da Senegal ta fi kwarewa wajen dafa shinkafa dafaduka

Muryar Amurka ta zagaya cikin jihar Oyo inda ta ji ra'ayoyin 'yan Najeriya da suka taba cin dafadukan kasashen uku.

Alhaji Uba Ahmed wanda aka tambayeshi akan wannan gaddamar bai yi wata wata ba yace Ghana ce tafi kwarewa. Yace sun fi Najeriya yin anfani da wasu abubuwa wurin dafa dafaduka. Suna sa tumatiri da ganye da busashen kifi da dai sauransu. Kodayake bai san ta Senegal ba amma ya ci ta Mali kuma yace bata da dadi kamar ta Ghana.

Hadiza mai Koko ita ma tace Ghana ce tafi yin dafaduka mai dandano saboda wai sun iya hada kayan sosai. Tace Senegal na yi amma basu kware kamar Ghana ba.Najeriya ma tana yi amma bata kai Ghana ba.

Shi ko Abu Leme Okada cewa yayi ba'a hada dafadukan Najeriya da ta Ghana ko Senegal. Ya ci duka na kasashen amma babu kamar Najeriya wadda ta fisu dandano.

Maryam mai sayar da abinci tace Najeriya ce tafi iya dafaduka.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG