Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Bukin Sallah Cikin Dokar Ta Baci


Musulmai na sallar Eid al-Fitr
Musulmai na sallar Eid al-Fitr

Jihohi uku a arewa maso gabashin Najeriya ke cikin dokar ta baci. Adamawa daya daga cikinsu jama'arta na shirin bukin sallah.

Tabarbarewa tsaro a arewa, musamman arewa maso gabashin Najeriya ya sa gwamnatin tarayya ta kakabawa jihohi uku, wato Adamawa, Borno da Yobe dokar ta baci. A cikin wannan halin ne jihohin suka shiga hidimar aikin ibada na azumi.

A jihar Adamawa, daya daga cikin jihohi uku dake karkashin dokar ta baci jama'a na kokarin shirin bukin sallar karshen azumi.Wakilinmu Ibrahim Abdulaziz Biu ya zagaya garin Yola babban birnin jihar Adamawa ya ga irin shirin da jama'ar jihar ke yi. Duk da dokar ta bacin ya ga teloli suna harkar dinkin salla kamar yadda suka saba can baya. Teloli da yawa sun samu aikin yi to amma ba duka bane ke darawa a wannan lokacin domin wasu sallar ta samesu a wani hali na rashin kudi. Wani magidanci Malam Garba Usman ya ce rashin biyan albashi na cikin dalilan da suka jawo masa rashin kudi a wannan lokacin. Ya ce dakyar suka iya yin kashi daya cikin kashi uku na abubuwan da suke yi da lokacin wadata. 'Yan kasuwa ma na kokawa. Wani mai sayar da tufafi ya ce sun sayo kaya amma babu masu saye domin rashin kudi.

Garin Yola ya soma cika da mutane har ma an soma karbar harami da bakin mahawa dawakai a fadar Lamidon Adamawa bikin salla kamar yadda aka saba yi.

Ibrahim Abdulazi Biu nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG