Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Bunkasa Ungozoma Na Samun Ci Gaba Sosai A Najeriya


Wata ungozoma tana bayyana wa mata irin matakan da zasu iya dauka domin rage kasadar mutuwa a sanadin ciki ko kuma haihuwa
Wata ungozoma tana bayyana wa mata irin matakan da zasu iya dauka domin rage kasadar mutuwa a sanadin ciki ko kuma haihuwa

Shirin da aka bullo da shi a 2009 ya samu nasara sosai wajen rage yawan mace-macen mata lokacin haihuwa tare da bunkasa yin rigakafi ga jarirai

A ranar 8 ga watan Mayu ne aka yi bukin ranar tuna uwa a fadin duniya. A Najeriya, daya daga cikin kalubale mafi muni da ake fuskanta shi ne na mutuwar uwaye mata lokacin haihuwa. Alkaluma sun nuna cewa a wasu sassan Najeriya, mata har dubu daya da dari biyar ne suke mutuwa, daga cikin mata kimanin dubu dari da suka haihu.

Domin takalar wannan kalubale ne ya sa Najeriya ta bullo da Shirin Bunkasa Ungozoma a shekarar 2009.

Wannan shirin yana dauko ungozomomi daga kowane lungu na Najeriya, wasu wadanda ba su da aikin yi, wasu wadanda suka riga suka yi ritaya, amma kuma su na da karfin da zasu iya taimakawa wajen karbar haihuwa.

Makasudin shirin shi ne samar da kafa ta toshe gibin da ake da shi na rashin wadatattun masu karbar haihuwa musamman a yankunan karkara.

Kowacce ungozomar da aka dauka, ana ba ta horaswa kan sabbin dabarun karbar haihuwa, sannan ana ba ta kayan aiki wadanda suka hada da, naurar sauraron numfashi ko motsi, reza, muhimman magunguna, sikelin auna nauyi, na'urar auna karfin bugun jini da kuma ta yin rajistar haihuwa.

Har ila yau, wadannan ungozoma su na gudanar da aikin yin allurar rigakafi ma jariran da aka haifa a asibitoci tare da taimakawa wajen gudanar da ayyukan tazarar haihuwa.

Wannan shirin ya nuna alamun sabon kuzari, kuma tuni har ya fara kawo bambanci wajen kyautata rayuwar uwaye mata a Najeriya. Babu shakka, wannan abin lura ne a yayin da jama'a suke murnar Ranar Tunawa da Uwa a wannan shekarar.

XS
SM
MD
LG