Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Habaka Abuja


Shugaban Najeriya a Abuja
Shugaban Najeriya a Abuja

Kawo yanzu kashi goma sha daya ne kawai na girman birnin da aka tsara. Yanzu ana wani shiri na kara wani kashi goma sha dayan

Yayin da ministan birnin Abuja ya kawo ziyara nan kasar Amurka abokin aiki Aliyu Mustaphan Sokoto ya samu ya zanta da shi.

A cikin firar tasu ministan ya ce ba China kadai suke muamala ba har da Ingila da wasu kasashen domin kara gina birnin Abuja. Ya ce ganin haka ya sa Amurka ta yi sha'awar shigowa. Yanzu zasu taimaki birinin da gyara yanayi da gina muhallai musamman na masu karamin karfi wajen matsuguni da kuma gidaje.

Akwai wani shiri kuma na musayar fili. Wannan in ji ministan shiri ne wanda za'a baiwa masu arziki katafaren fili su sa ma'adanai kamar hanyoyi, wutar lantarki da ruwa da dai makamantansu ya kasance da mutum ya zo kawai sai dai ya gina filinsa ya shiga. Daga filin wadanda suka saka ma'adanan zasu dauki kashi 60 kana gwamnati ta bayar da sauran kashi 40 wanda z'a baiwa marasa karfi wato talakawa da sauran ma'aikata. Filayen za'a gina gidaje da makarantu da asibitoci da wuraren kasuwanci.

Dama a cikin tsarin Abuja gundumomi 83 za'a gina. Amma kawo yanzu duk da girman kashi goma sha daya kawai aka gina. Amma yanzu da taimakon manyan 'yan kasuwa goma sha biyar za'a kara gina gudumomi goma sha daya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG