Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Trump Na Ragewa Amurkawa Haraji


Shugaba Donald Trump ya yi kiran da a yi ragi mai yawa a haraji ga bangaren masana’antun Amurka, don samar da ayyukan yi ga kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a duniya, kuma ayi gyare-gyare masu yawa a dokokin harajin kasar da zai shafi miliyoyin Amurkawa masu biyan haraji.

Shawarar da shugaba Trump ya bayar na rage haraji a kan masana’antu Amurka, kasa mafi karfin masana’antu a duniya, daga kashi 35 zuwa kashi 15 cikin dari.

Ya kuma yi kiran da a kawo ribar cinikin da masana’antun Amurka dake kasashen waje ke samu, matakin da sakataren bitalmalin kasar Steven Mnuchin yace zai shigo da triliyoyin dala zuwa gida Amurka don fadada kasuwancin a cikin gida.


Samar da ayyukan yi da habbaka tattalin arziki abu ne mai muhimmanci inji babban mai bada shawara a kan tattalin arziki a fadar White House Gary Cohn, wanda ya taba zama jami’in kudi a cibiyar hada hadar kasuwanci ta Wall Street. Yace babban manufarmu itace saukaka biyan haraji, rage tsadar kaya da yin sauki.

Yace ba wai muna nufin musguna ma wani bane. Muna niyyar tabbatar da adalci ne a kasar kana muna nufin karfafa zuba jari a cikin kasar.


Mnuchin ya kira wannan ragowar haraji amfi girma a tarihin Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG