Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Somaliya Ya Mika Kokon Barar Sa Sakamakon Fari Da Ya Addabi Kasar


Sabon shugaban kasar Somalia ya mika kokon bararsa ga kasashen duniya da su tallafawa kasar kan yadda zata kaucewa farin dake daf da dunfarar kasar sa.

Yace kusan rabin mutanen kasaer tasa suna fama da karancin abinci kana kashi 15 daga cikin 100 suna fuskantar barazanar fari.

Shugaba Mohammed Abdullahi, wanda ake wa lakabi da Farmajo, yana wannan Maganar ce sa’ilin da yake wa taron tsaro na majalisar dinkin duniya jawabi.

Yace a Gaskiya ina mai cike da bakin ciki na irin wannan halin da kasa ta ta shiga, domin ko mutanen kasar Somalia, mutane ne masu alfahari, da kwazo kana mara sa kasala.

Yace sune mutane na karshe da zasu nemi taimako inda ace akwai hanyar da zasu bi domin su samu nakansu maimakon ace sun tsaya roko.

Shugaban wanda ya kama ragamar mulkin kasar a cikin watan da ya gabata, yace mutanen kasar suna aiki na tsawon sa’oi masu yawa domin kawai neman abinci da ruwa, Wannan yasa da yawan dabbobi sun mutu sanboda tsananin fari, kana cutar kwalara kuma sai kara ta’azzara take yi.

Ba shakka kasar ta Somalia, it ace tasan tsananin abinda fari ke haifarwa domin ko mutane sama da 260 ne suka mutu sakamakon wannan farin a cikin shekar 2011 da wannan lamnari ya rutsa dasu, Kuma yanzu haka mutane da yawansu yakai miliyan 6 ke bukatar taimako.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG