Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Assad Ya Lashi Takobin Murkushe 'Yan Ta'adda


Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham, wanda ya lashi takobin kawar da abinda ya kira 'yan ta'adda daga kasar
Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham, wanda ya lashi takobin kawar da abinda ya kira 'yan ta'adda daga kasar

Shugaban na Sham ya lashi takobin raba kasar da 'yan ta'adda yayin da dakarunsa ke ci gaba da gwabzawa da 'yan tawaye a Aleppo da Damascus

Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham ya lashi takobin raba kasar da abinda ya kira "'yan ta'adda" a yayin da dakarun tsaro suke ci gaba da gwabzawa da 'yan tawaye wadanda suka yi kokarin kwace wasu sassan biranen Aleppo da Damascus.

Kafofin yada labarai na gwamnatin Sham sun ambaci shugaba Assad yana fadi jiya talata cewa ba zai nuna sassauci ga 'yan ta'adda ba. Ya gana da sakataren Majalisar Tsaron kasa ta Iran, Saeed Jalili, wanda ya kai ziyara kasar ta Sham.

Gidan telebijin na kasar Sham ya nuna ganawar tasu, wanda kuma shi ne karon farko da aka ga shugaba Assad a telebijin cikin makonni biyu.

Jalili yayi alkawarin cewa Iran zata ci gaba da goyon bayan kasar Sham, wanda yace tana daya daga cikin ginshikan yin adawa da abokan gaba na kasashen waje.
XS
SM
MD
LG