Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Karrama Wasu Tsoffin Sojoji da Suka Nuna Jarumtaka


Shugaba Barack Obama yana karrama Saje Bennie G. Adkins
Shugaba Barack Obama yana karrama Saje Bennie G. Adkins

Bayan kusan shekaru arba'in da karwar yakin Vietnam shugaban Amurka ya karrama wasu jaruman sojoji biyu jiya a fadarsa.

Bayan kusan shekaru 40 da kare yakin Vietnam shugaban Amurka Barack Obama ya bada lambar yabo mafi daukaka a aikin soja ga saje-manjo Bennie Adkhins mai ritaya da wani soja Donald Sloat.

Majalisar dokokin Amurka ta amince da a bada wannan lambar yabo, domin bisa ka’ida duk soja da za’a karrama saboda wata bajinta tilas a yi haka cikin shekaru biyu da nuna jaruntakar.

Shugaba Obama yace da samun sabbin shaidar , dai dai ne da aka sake duba lamarin kuma aka bada lambobin yabon.

Mr. Obama yace cikin shekaru da suka wuce tsoffin sojoji da suka yi yakin Vietnam ba sa samun girmawa data cancanta. Shugaban na Amurka yace tsoffin sojojin masu kishin kasa ne da suka nuna bajinta kuma Amurka tana alfahari dasu.

An karrama Bennie Adkhins saboda kukan kura da yayi a 1966 na ceto wani soja da ya jikkata yayinda abokanan gaba suke ruwan wuta akansu.

Shi kuma Donald Sloat ya mutu ne a fagen daga a 1970 lokacinda ya maida gangar jikinsa a zama garkuwa wajen kare ‘yan uwansa sojoji daga wata nakiya wacce ta halakashi.

XS
SM
MD
LG