Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Ba Mitt Romney Rata...


Shugaba Barack Obama
Shugaba Barack Obama

Sabuwar kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a ta nuna cewa a karon farko shugaban na Amurka yana gaban mutumin da ake jin cewa shi ne zai zamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican

Wata sabuwar kuri'ar neman ra'ayoyin jama'a ta nuna cewa, a karon farko, shugaba Barack Obama na Amurka, ya wuce gaban mutumin da ake ganin zai zamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney, idan da za a yi zabe yau.

Kuri'ar wadda gidan telebijin na ABC News da jaridar Washington Post suka gudanar, ta nuna cewa idan shugaba Obama zai kara da Romney ne, zai samu kashi 52 cikin 100, yayin da shi dan takarar na jam'iyyar Republican zai samu kashi 43 cikin 100, watau tazarar maki 9. Wannan kuri'ar da aka gudanar a makon da ya shige, ta nemi jin ra'ayoyin mutane dubu daya, balagaggu, wadanda rabinsu suka bayyana cewa sun gamsu da irin aikin da shugaban ke gudanarwa, kuma ya cancanci wa'adi na biyu kan mulki.

Mitt Romney, mutumin dake kan gaba cikin masu neman takarar kujerar shugaban Amurka a inuwar jam'iyyar Republican
Mitt Romney, mutumin dake kan gaba cikin masu neman takarar kujerar shugaban Amurka a inuwar jam'iyyar Republican

A cikin wata hirar da aka yi da shi a telebijin ran lahadi, shugaba Obama ya ce ya cancanci a sake zabensa, yana mai misali da sabbin alkaluman dake nuna tattalin arzikin Amurka ya fara samar da karin ayyukan yi. Ya fadawa gidan telebijin na NBC cewa tattalin arzikin Amurka yana bunkasa fiye da yadda ya samu shekaru uku da suka shige, koda yake har yanzu da sauran aiki a gaba.

Shugaban yayi nuni da cewa rahoto ya nuna cewa a wata na biyar a jere, ana samun raguwar rashin aiki a Amurka, inda a watan Janairu kadai aka samu karin ayyukan yi guda dubu 250. Yace a shekarar 2009 lokacin da ya fara mulki, a kowane wata, ana hasarar ayyukan yi da yawansu ya ninka wannan har sau uku.

Amma masu kwadayin jam'iyyar Republican ta tsayar da su takarar kujerar shugaban kasa sun ce tattalin arzikin ba ya farfadowa da saurin da ya kamata, kuma manufofin Mr. Obama sun kasance marasa nagarta.

XS
SM
MD
LG