Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Jagoranci Tawagar Amurka Zuwa Bikin Jana'izar Nelson Mandela


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Za'a binne Nelson Mandela ranar 15 ga watan Disamba amma tun yau aka fara bikin jana'izarsa lamarin da ya sa Shugaba Obama ya jagoranci tawagar Amurka zuwa Afirka Ta Kudu

Shugaban Amurka Barack Obama da uwarginsa Michelle Obama da tsoffin shugabannin kasar da suka hada da Geroge W. Bush da Bill Clinton da Jimmy Carter duk suka nufi Afirka Ta Kudu domin halartar bikin jana’izar tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela wanda ya rasu ranar Alhamis da ta gabata.

Tsohon shugaba George H. W. Bush mahaifin tsohon shugaba George W Bush shi ne kadai ba zai samu zuwa Afirka Ta Kudu ba sabili da tsufan jiki. Mai magana da yawunsa ya ce tsohon shugaban mai shekaru tamanin da tara da haihuwa baya iya doguwar tafiya yanzu.

Sakataren Harkokin Wajen Afirka Ta Kudu Maite Knoana-Mashabane ya ce shugabannin duniya masu dimbin yawa fiye da tsammani suka nuna sha’awar halartar bikn jana’izar domin su karama gwarzon namuji da ya yaki mulkin wariyar fata lamarin da ya kaishi gidan kaso har na tsawon shekaru dai dai har ashirin da bakwai.

Cikin mahalartan har da Firayim Ministan Biritaniya David Cameron da shugaban Iran Hassan Rouhani da na Cuba Raul Castro da babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon. Duk zasu halarci jana’izar mutumin da ya kwashe shekaru 27 a gidan kaso daga bisani ya dawo ya zama shugaban kasar farar fata na farko.

Shahararriyar mai shirin tattaunawa a kafar telibijan Oprah Winfery da shahararren mawaki dan kasar Ireland Bono da ginshakin attajirin kasar Biritaniya Richard Branson duk zasu kasance a wurin.

Shugabannin duniya da wadanda suka yi suna a duniya zasu hadu da masu juyayin mutuwar Nelson Mandela daga sassa daban daban a katafaren filin wasan kwallon kafa na Jahannesbourg.

Za’a ajiye gawar Mandela a ginin Union a Pretoria fadar gwamnatin kasar daga ranar Laraba zuwa Juma’a.

Za’a kammala bukukuwan da jana’izar Mr Mandela ranar 15 ga watan Disamba a mahaifarsa dake kauyen Qunu.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG