Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Yace Amurka Ta Sare Kan Al-Qa'ida


Shugaba Barack Obama yana jawabi ga sojojin da suka komo daga Afghanistan a sansanin mayaka na Fort Campbell dake Jihar Kentucky, Jumma'a 6 Mayu, 2011
Shugaba Barack Obama yana jawabi ga sojojin da suka komo daga Afghanistan a sansanin mayaka na Fort Campbell dake Jihar Kentucky, Jumma'a 6 Mayu, 2011

Shugaban na Amurka yace mutumin da ya jagoranci hare-haren 11 ga watan Satumbar 2001 ba zai sake yin barazana ga Amurka ba har abada

Shugaba Barack Obama ya ce Amurka ta “sare kan” kungiyar al-Qa’ida a bayan da ta kashe Osama bin Laden, kuma ko ba dade ko ba jima zata gama da kungiyar.

Mr. Obama ya fada jiya jumma’a cewa a saboda “kwarewa da jarumtaka” na mutane da dama, mutumin da ya jagoranci hare-hare kan Amurka ranar 11 ga watan Satumbar 2001, ba zai sake yin barazana ga Amurka ba har abada.

Shugaba Obama yayi wannan furuci nasa a sansanin sojoji na Fort Campbell dake jihar Kentucky, a bayan da ya gana a kebance da zaratan sojojin da suka kai farmaki kan gidan da bin Laden ya buya ciki a ranar litinin suka kashe shi.

A jawabin da yayi a Fort Campbell, Mr. Obama yace ya fadawa zaratan sojojin cewa sun yi aikinsu yadda ya kamata.

Shugaba Obama yayi jawabin ne ga daruruwan sojojin da suka komo kwanakin baya daga aiki a kasar Afghanistan. Yayi musu marhabin da komowa ya kuma yaba musu saboda aikinsu. Har ila yau, yace ana samun ci gaba a kokarin tarwatsawa da murkushe kungiyar al-Qa’ida.

XS
SM
MD
LG