Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Yace Indonesiya Abar Koyi Ce Ga Sauran Duniya


Shugaba Obama yana jawabi yau laraba, 10 Nuwamba, 2010 a Jami'ar Indonesiya a birnin Jakarta.
Shugaba Obama yana jawabi yau laraba, 10 Nuwamba, 2010 a Jami'ar Indonesiya a birnin Jakarta.

Shugaban na Amurka ya yaba da zaman lumana da mutunta addinai da ake yi a a kasar da ta fi kowacce yawan Musulmi a duniya, Indonesiya

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yaba da mulkin dimokuradiyya da kuma jurewa addinai dabam-dabam da kasar Indonesiya take yi, yana mai fadin cewa kasar, wadda ta fi kowacce yawan Musulmi a duniya, abar misali ce ga sauran duniya.

A cikin wani muhimmin jawabin da yayi a Jakarta, shugaba Obama yace zaman lumanar da addinai suke yi a kasar na daya daga cikin muhimman dabi’u na Indonesiya. Yace Indonesiya da Amurka su na da akida guda cewar bambancin addini da na al’ada, karin karfi ne ga kasa.

Mr. Obama yace Amurka ba ta yaki da addinin Musulunci, kuma har abada ba zata yaki Musulunci ba.

Shugaban na Amurka ya lashi takobin ci gaba da kokarin ganin an samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, duk da abinda ya kira, manya-manyan matsaloli.

Ziyarar shugaba Barack Obama zuwa Indonesiya, sake komawa kasar da ya shafe shekaru 4 yana zaune cikinta ne lokacin yana dan yaro a shekarun 1960. Shugaba Obama ya fada yau laraba da harshen mutanen Indonesiya cewa kasar wani bangare na jikinsa ne.

Wannan jawabi da shugaba Obama yayi a Jami’ar Indonesiya dake Jakarta ya tabo wasu daga cikin batutuwan da ya bayyana cikin jawabinsa na bara ga al’ummar Musulmin duniya a al-Qahira a inda yayi kiran da a samu mutunta juna a tsakanin Amurka da kasashen Musulmi. Shugaba Obama ya fada yau laraba cewa dangantaka a tsakanin Amurka da kasashen Musulmi ta yi shekaru da dama tana tabarbarewa. Yace a matsayinsa na shugaban kasa, ya bayar da muhimmanci ga kokarin gyara wannan dangantaka da kasashen Musulmin.

Tun fari a yau laraba, shugaba Obama ya ziyarci Masallacin Istiqlal na Jakarta, masallacin da ya fi kowanne girma a duk fadin yankin kudu maso gabashin Asiya.

XS
SM
MD
LG