Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Bai Rufe Mijami'ar Dake Fadarsa Ba


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Fakewa da addini ko bangaranci ba shi ne zai kawowa kasar Najeriya cigaba ko nasara ba

Babban sakataren kungiyar hadin kan kiristocin arewacin Najeriya Pastor Simon Donli ya halarci taron gaggawa domin marawa shugaba Buhari baya bisa ga mukaman da ya nada cikin kwanaki dari yana rike da mulkin Najeriya.

'Yan kungiyar sun musanta wata jita-jita da ta kunno kai cewa wai an rufe mijami'ar dake fadar shugaban kasa. Pastor Donli yace mutane ne masu neman hanyar bata gwamnatin Buhari suke rubuce rubucen banza da wofi wadanda basu kamata ba

Mataimakin shugaban kasa a nan cikin mijami'ar yake sujada. Karya ake shatawa saboda a kawo rashin zaman lafiya domin a ce shugaba Buhari baya son kirista. Pastor Donli yace kada a hada siyasa da addini domin yin hakan zai iya kawo tashin hankali.

A cewar Pastor Donli yanzu a arewa babu maganar cewa wannan musulmi ne wancan kirista ne. Yace duk an zama daya kuma kirista da musulmin arewa zasu yi tafiya daya.Yace suna farin ciki da zuwan shugaba Buhari domin ba'a taba yin kakakin majalisar wakilai daga arewa kirista ba. Haka kuma ba'a taba yin sakataren gwamnatin tarayya kirista daga arewa ba sai a wannan karon. Tunda shugaba Buhari zai ba kirista mukamin sakataren gwamnati yaya za'a ce baya son kirista?

Kwanaki dari da shugaba Buhari yayi akan mulki na samun suka da yabo. Shugban jam'iyyar adawa ta kwadago, wato Labor Party Abdulkarim Abdulsalami yace babu wata nasara da shugaba Buhari ya samu cikin kwanaki darin da yake mulki. Yace kwanaki darin sun jawo wahala domin talakawa sun fara kuka. Wai ci da sha sun gagari mutane.

Shi kuwa jigon APC Inuwa Yahaya yace su kam sun ga nasarori da dama. Alama ta nuna kasar na kan hanyar samun nasara. Idan a ka baiwa shugaban kasa hadin kai za'a kaiga tudun mun tsira. Gyara da shugab zai yi sai ya kama daga sama har kasa.

Dangane da nada sabbin ministoci Barrister Bello Rigachukun yace sai an kawar da kai. A dauko wanda za'a iya wankewa saboda taimakon da zai kawowa kasa a kuma guji wanda zai rusa kasar.

Shi ma Sanata Goje yace ya zama wajibi kowa ya yi kishin kasa tare da ba gwamnati damar sauyin da ake bukata.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG