Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Ya Sassauta Ka'idojin dake Tauye Kungiyoyin Addini.


Trump A Yayin Da Yake Gabatar Da Dokar Insuran Kiwon Lafiya
Trump A Yayin Da Yake Gabatar Da Dokar Insuran Kiwon Lafiya

Shugaba Donald Trump na Amurka ya sassauta ka’idojin dake tauye kungiyoyin addini wadanda basa biyan haraji daga shiga hidimomin dake da alaka da siyasa.

A jiya Alhamis ne Trump ya saka hannu akan wata dokar da ta baiwa Hukumar Tara Haraji ta I-R-S damar daukan matakin da ta ga “ya cancanta amma ba haramtawa” kungiyoyin addini dake shiga kungiyoyin siyasa da harkokin siyasa.

Duk da cewa dama can akwai wannan dokar, ba kasafai IRS ke aiwatar da ita ba.

A jawabinsa lokacinda yake rattaba hannu akan dokar a jiyan, shugaba Trump ya lura da yadda ake wa shugabannin addinin Kiristoci da na Musulmi barazana a duk lokacinda aka ji suna magangannun da suka shafi siyasa.

Don haka a jiyan ya umurci IRS da cewa kada ta sake aiwatarda wannan dokar ta Johnson, wacce ta haramta wa kungiyoyin addini nuna goyon bayansu ga wani dan takaran mukami na siyasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG