Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Laurent Gbagbo Yace Bai Yarda Da Sakamakon Zaben Fitar Da Gwani Ba


Jami'in jam'iyyar shugaba Laurent Gbagbo a hukumar zaben Ivory Coast, yana keta sakamakon zaben da kakakin hukumar ya zo bayyanawa a gaban 'yan jarida.
Jami'in jam'iyyar shugaba Laurent Gbagbo a hukumar zaben Ivory Coast, yana keta sakamakon zaben da kakakin hukumar ya zo bayyanawa a gaban 'yan jarida.

Jami'an jam'iyyar shugaba Gbagbo sun hana jami'an hukumar zaben kasar Ivory Coast fadin sakamakon zaben da suka ce an yi magudinsa ne.

Wakilan shugaba Laurent Gbagbo na kasar Ivory Coast ko Cote D'Ivoire, sun hana jami’an zabe na kasar bayyana sakamakon farko daga zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka gudanar ranar lahadin da ta shige.

Jiya talata da maraice, kakakin hukumar zabe ta kasar, Bamba Yacouba, ya fito zai karanta sakamako mai yawa da aka samu, sai jami’an jam’iyyar shugaba Gbagbo suka shigo a fusace suka kwace takardun da yayi niyyar karantawa.

Wani wakilin hukumar zaben daga jam’iyyar shugaba Gbagbo, Damana Picasse, ya kekketa takardun sakamakon a gaban ‘yan jarida, ya kuma ce ba na halal ba ne.

Tun da fari, wani wakilin dan takarar hamayya Alassane Ouattara, ya zargi shugaba Gbagbo da laifin hana hukumar zaben gudanar da ayyukanta tare da kokarin kwace mulki.

Amurka ta yi kira ga ‘yan takarar shugaban kasar da su kyale a kidaya kuri’un a kuma bayyana sakamakon ba tare da tsangwama ba, sannan ta bukace su da su mutunta duk sakamakon da hukumar zata bayyana. A cikin wata sanarwa da ta bayar jiya talata, sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce zaben wata dama ce ga kasar ta CI ta tsamo kanta daga cikin rikicin da ta fada na shekaru.

XS
SM
MD
LG