Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Gana Da Bukola Saraki


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawa da shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki, inda suka tattauna akan muhimman abubuwan da suka shafi gudanar da mulki a Najeriya.

Koda shike irin wannan ganawa ba sabuwar abu bace domin kuwa dukkan bangarorin biyu, ‘yan jam’iyya daya ne dake mulkar al’umma daya, amma ana ganin ganawar ta zo a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya, ke da bukatu da dama daga shugabannin biyu.

Bayan an kammala ganawar ne shugaban majalisar ya yi wa manema labarai jawabi inda ya bayyana cewa ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari, bayani ne akan kasafin kudi da kuma sababbin dokokin da majalisa ta amince da su musamman akan sha’anin zabe.

To amma ko mai yasa ba a tattauna akan batutuwan da suka shafi majalisa ba, da kuma ja-in-ja dake ake da bangaren gwamnati? Tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Umar Faruk Musa, Kenan ya yiwa kakaki a fadar shugaban majalisar dattawa Mohammed Isa Funtua, inda ya bayyana cewa shugaban kasa ya riga ya kafa kwamitin da zai fuskanci wannan lamarin.

Ga cikakken rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG