Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka ya yi magana kan tattalin arzikin kasar da batun kasar Libya da kuma Afghanistan


Shugaban Amurka Barack Obama yana masa tambayoyi a taron manema labarai,
Shugaban Amurka Barack Obama yana masa tambayoyi a taron manema labarai,

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi magana dangane da tattalin arzikin Amurka da batun Libya.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi magana dangane da tattalin arzikin Amurka da batun Libya da kuma Afghanistan a wani taron manema labarai da ya gudanar a fadar White House yau Laraba. Mr. Obama ya yi kira ga majalisa ta dauki mataki da yace zai bunkasa tattalin arzikin kasar ya kuma taimaki Amurkawa, da ya hada da inganta huldar kasuwanci da Colombia da Panama da kuma Koriya ta Kudu. Yace tilas ne majalisa ta dauki mataki cikin sauri na kayyade bashin da ake bin gwamnati, yayinda kuma ake rage gibin kasafin kudin Amurka. Dangane da Libya, ya kare matakin kasa da kasa da ake dauka na tsawon watanni uku, da cewa, daukar wannan matakin ya taimaka wajen kare dubban mutanen kasar dake arewacin Afrika. Ya bayyana cewa shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi yana bukatar sauka daga karagar mulki domin kare lafiyar mutanen kasar Libya. Mr. Obama ya kuma maida martani dangane da kushewa batun Libya da majalisa ke yi , da cewa bai sabawa kudurin ikon yaki ba, wata dokar da ta bukaci amincewar majalisa cikin kwanaki 60 idan dakarun Amurka suka shiga yaki. Dangane kuma da Afghanistan shugaba Obama yace, Amurka tana taka tsantsa wajen janye dakarunta, zata kuma ci gaba da matsawa kungiyar al-Qaida lamba, ko bayan dakarun Amurka sun fice daga kasar. Bisa ga cewarshi, alheri ne ga Amurka idan ba a bari gwamnatin kasar Afghanistan ta fadi ba, sabili da wannan zai sake ba kungiyar Taliban damar yin karfi. Yace za a janye dakarun ne bayan an shafe tsawon shekaru goma ana yaki.

XS
SM
MD
LG