Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Zai Bayyana Sabbin Matakan Taimakawa Yakar Cutar Ebola


Shugaban Amurka Barack Obama akan cutar ebola
Shugaban Amurka Barack Obama akan cutar ebola

Yau Talata Shugaban Amurka zai kai ziyara a cibiyar hana yaduwar cututtuka dake Gerogia inda kwararru zasu fadakar dashi akan cutar kana ya bayyana sabon shirin yaki da cutar a yammacin Afirka.

A kokarin ci gaba da yaki da cutar Ebola, yau talata ake sa ran shugaban Amurka Barack Obama zaiyi balaguro zuwa helkwatar cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka dake Georgia, inda zai saurari bayanai daga masana kiwon lafiya gameda annobar Ebola a yammacin Afirka.

Jami’an fadar white House sun ce Mr. Obama a lokcin ziyarar a Atlanta zai bada sanarwar sabbin matakai da gwamnatin Amurka zata dauka na taimakawa a yaki da wannan cutar, wacce tuni ta halaka fiyeda mutane dubu biyu da dari hudu a yammacin Amurka.

Kakakin fadar white Josh Earnest ya fada jiya litinin cewa saboda karfin Amurka tana wani hakki na musamman ta zabura wajen shawo kan wannan annoba.

Zuwa yanzu Amurka ta ayyana dala milyan dari daya domin yaki da wannan cuta kuma ta tura ma’aikatan kiwon lafiya 100 zuwa yammacin Afirka. Duk da haka wasu shugabannin kasashen Afirka sun ce matakin da Amurka ta dauka kan wannan cutar bai wadatar ba.

Jami’an difilomsiyya sun ce kwamitin sulhu na MDD zai yi taron gaggawa kan cutar Ebola ranar Alhamis. Wannan shine karo na biyu da kwamitin zaiyi zama kan kiwon lafiya. Tayi irin wannan zama dangane d a cutar kanjamau a shekara ta 2000.

XS
SM
MD
LG