Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka zai kai ziyara kasar Cuba


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka, ya tabbatar dazun nan cewa zai kai ziyara zuwa kasar Cuba a wata mai zuwa, domin karfafa ci gaban da aka samu a dangantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma kokarin inganta rayuwar al’ummar kasar Cuba.

A lokacin da yake bayyana wannan ta shafin Twitrter, Obama ya lashi takobin tado da batutuwan kare hakkin bil Adama a tattaunawar da zai yi da jami’an gwamnatin kasar mai bin tafarkin kwaminisanci.

Wata sanarwar fadar White House kuma ta ce wannan ziyara mai dimbin tarihi, wadda it ace ta farko da wani shugaban Amurka zai kai kasar Cuba a cikin shekaru kusan casa’in, karin alama ce ta kudurin shugaba Obama na shata sabuwar turbar dangantaka tsakanin Amurka da Cuba, tare da kusanto da al’ummar kasashen biyu ga junansu ta hanyar tafiye-tafiye, kasuwanciu da kuma samar da bayanai.

Sanarwar ta ce Obama zai fara ziyarar kwanaki biyu a Cuba dsaga ranar 21 ga watan Maris kafin ya zarce zuwa Argentina.

Wannan ziyara zuwa kasar Cuba ta nuna cewa shugaba Obama ya kuduri aniyar ci gaba da abinda yake gani a zaman wata babbar nasarar da gwamnatinsa ta samu kafin ya sauka daga kan wannan kujera nan da shekara daya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG