Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Hamayya Na Burundi Ya Bayyana Dalilan Buyar Da Yayi


Agathon Rwasa
Agathon Rwasa

Tsohon madugun 'yan tawaye Agathon Rwasa ya ce gwamnati tana neman kama shi bisa zargin cewa yana kokarin sake tayar da tawaye.

Wani babban jagoran 'yan hamayya a kasar Burundi ya fitar da sanarwar da aka dauka kan faifai inda yake bayyana dalilansa na gudu da kuma buya a makon da ya shige.

A wannan sakon da ya karanta cikin kaset da aka ba 'yan jarida, Agathon Rwasa ya ce gwamnati tana shirin kama shi bisa zargin cewa yana shirya kaddamar da sabon tawaye a kasar.

Ya ce ana wannan kulle-kullen a kansa ne a saboda ya jagoranci 'yan hamayya wajen zargin cewa an yi magudi a muhimmin zaben yankuna da aka yi a watan Mayu.

Kimanin mako guda da ya shige ne Rwasa ya bace daga gidansa dake Bujumbura, babban birnin kasar

Hukumomin Burundi sun ce ba a bayar da takardar iznin kama shi ba. Amma Rwasa ya ce gwamnatin ta tura 'yan leken asirinta su na farautarsa a kasar Kwango-ta-Kinshasa, inda ake tsammanin ya gudu ya buya.

Jam'iyyar FNL ta Rwasa ita ce ta zo ta biyu a zaben gundumomin da aka yi a ranar 24 ga watan Mayu, zaben da aka zub da jini a lokacinsa. Dukkan jam'iyyun hamayya na kasar sun ki yarda da sakamakon zaben.

Daga baya, jam'iyyun na hamayya sun kaurace wa zaben shugaban kasar da aka yi ranar litinin da ta shige, inda aka bar shugaba Pierre Nkurunziza shi kadai a matsayin dan takara ba tare da hamayya ba.

XS
SM
MD
LG