A lokacin da ya ke ganawa da shugabannin jam’iyar MPLA a Luanda babban birnin Angola, Santos ya ce zai ajiye harkar siyasa baki daya.
A watan Satumbar shekarar 2017 wa’adin Santos zai kare, sai dai shugaban bai ambaci dalilin da ya sa zai sauka daga mulki a shekarar ta 2018 ba, sannan bai fadi maksudin shirin na sa na yin ritaya ba.
Dan shekaru 73, Dos Santos ya kasance a akan karagar mulki tun daga shekarar 1979.
Shi ne na biyu a jerin shugabannin Afrika da suka fi dadewa akan mulki, bayan Teodoro Obiang Nguema na kasar Equatorial Guine.
Masu sukan shugabancinsa, suna zarginsa da yin amfani da mukaminsa wajen azurta kansa da abokanansa da kuma iyalansa ta hanyar wawure kudin man kasar.