Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Ghana zai kawo ziyara fadar White House ta Amurka


Shugaban Ghana John Atta Mills
Shugaban Ghana John Atta Mills

Shugaba John Atta Mills na kasar Ghana yana shirin ganawa da shugaba Barack Obama na Amurka yau alhamis a fadar White House

Shugaba John Atta Mills na kasar Ghana yana shirin ganawa da shugaba Barack Obama na Amurka yau alhamis a fadar White House dake nan Washington domin tattaunawar da Ghana ta ce za ta kara karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.

Darektan yada labarai na shugaba Mills, Koku Anyidoho, ya fadawa Muryar Amurka cewa shugabannin biyu zasu tattauna hanyoyin bunkasa ayyukan raya kasa da kuma huldar tattalin arzikin dake tsakaninsu.

Wannan ziyara tana zuwa ‘yan kwanaki kadan a bayan da kasar Ghana ta yi bukukuwan cikar shekaru 55 da samun ‘yancin kai, kuma shekaru 2 a bayan da shugaba Obama ya ziyarci kasar Ghana a ziyararsa ta farko zuwa Afirka a matsayin shugaban kasa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG