Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Guinea Alpha Conde Na Kan Hanyar Sake Lashe Zabe


A kasar Guinea mutaane suna kan layi suna jira su kada kuri'unsu
A kasar Guinea mutaane suna kan layi suna jira su kada kuri'unsu

Biyo bayan janyewar da dan hamayya Cellou Dalein Diallo ya yi daga takarar shugabancin kasar Guinea shugaba Alphan Conde zai lashe zaben da gagarumar nasara.

Da alama shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya kama hanyar sake lashe kuri'un da ake gaddama akai bayan da babban abokin hamayyarsa yace zai janye daga takarar.

Tunda aka riga aka kidaya kusan kashi tamanin na kuri'un da aka kada a zaben ranar Lahadi da ta gabata a wannan kasa dake Yammacin Afirka shugaba Conde zai lashe zaben da gagrumar nasara.

Ana kyautata zaton za'a bada sakamakon zaben gaba daya yau Juma'a.

Babban abokin hamayyar shugaban Cellou Dalein Diallo ya janye daga takarar ranar Laraba yana cewa ba zabe aka yi ba magudi aka tafka. Kawo yanzu ba'a sani ba ko janyewarsa zata tilasta a yi zaben zagaye na biyu.

Jiya Alhamis kungiyar Human Tights Watch ta gargadi jam'iyyun siyasa da su yi taka tsantsan su kaucewa tashin hankali. Kungiyar ta kuma kira jami'an tsaro su tabbatar babu tashin hankali ko karya doka da oda.

Dama ita kasar Guinea ta yi kamarin suna wajen tashin hankali da harzuka zaman dar dar bisa ga kabilanci lamarin da ya kan hallaka mutane da dama saboda rigingimun siyasa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG