Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Masar El'sissi Ya Zanta Da David Kemron Kan Matakan Tsaro


Shugaban kasar Masar da Firaministan Birtaniya sun yarda da tsaurara matakan tsaro a wajen yawon shakatawar nan na Sharm El-Sheikh, wajen da ya zama mafarin wajen da jirgin yakin Rasha ya fada a yankin Sinai a ranar Asabar da ta gabata.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga ofishi Firaministan Birtaninyar cewa, David Kemron da shugaban Masar Abdelfattah El’sissi sun tattauna ta waya gabanin ziyarar da zai kai birnin London.

Sun yarda da tsaurara matakan tsaron a filin jirgin saman da ke wajen shakatawar a Misira. Har yanzu dai ba wasu dalilan da aka bayyana na sanadiyyar hatsarin jirgin da ya hallaka mutane 224.

Wata na’urar tauraron dana dam din sojojin Amurka ta kyallaro hasken faduwar jirgin da ya fada yankin na Sinai.

Hukumomi dai suna kyautata zato an harbi jirgin da makami mai linzami ne kafin ya tarwatse ya fada nesa da tazarar kilomita 9,400 a saharar Sinai. Tuni dai jami’ar Masar suka shiga binciken musabbain faduwar jirgin.

Shugaban Masar ya yi watsi da jita-jitar cewa ‘yan kungiyar ISIS ne suka harbor jirgin kamar yadda ake yadawa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG