Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijar Ya Musanta Aniyar Yin Tazarce Zuwa Wa'adin Mulki Na Ukku


Shugaban Nijar Mohamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mohamadou Issoufou

Shawarwarin da majalisar dake warware maganganun siyasa a kasar Nijar kan bukatar aiwatar da gyaran fuska wa dokokin zabe ya sa wasu na ganin wani shiri ne na ba shugaban kasar daman yin tazarce zuwa wa'adin mulki na ukku a shekarar 2021.

Furucin da shugaban kasa Issoufou Mohamadou yayi yayin da ya cika shekara daya na soma wa'adin mulki karo na biyu ya cire tunanen yin tazarce a zukatan wasu 'yan siyasa.

Irinsu Sumaila Ahmadou shugaban jam'iyyar PND yana mai cewa shi kansa ya zargeshi da cewar da wuya mutum ya bar mulki. Yace baicin hakan akwai mutane dai dai manyan 'yan siyasa da suka yi taro dasu da suka tsayar cewa take-taken Shugaba Issoufou Mohammadou ba na barin mulki ba ne. Yace amma tunda ya fito ya bayyana cewa ba zai yi tazarce ba sai a bar maganar haka saboda ya zuba mata ruwa inji Sumaila.

To sai dai akwai banbancin ra'ayi tsakanin 'yan siyasa da masu rajin kare dimukradiya. Misali, mataimakin wata kungiyar kare dimukradiya Dauda Tankawa na kafa-kafa da kalaman Shugaba Issoufou Mohammadou.Yace su yanzu zasu rututa abun da yace su ajiye har Allah ya kai kasar ga lokacin zabe a sannan ne gaskiya zata fito.

A shekarar 2009 kasar Nijar ta shiga wani halin hayaniyar siyasa lokacin da Shugaba Tanja Mammadu ya nemi yin tazarce karo na ukku sabanin abun da kundun tsarin mulkin kasar ya kayyade. Dalili ke nan da wasu ke ganin a harkar siyasa komi na iya faruwa musamman idan aka ci karo da fadawa masu zuga shugaba. Inji Sumaila idan aka zuga mutum yana iya fita hankalinsa yayi abun da ba daidai ba.

Sumaila ya kara da cewa Tanja Mammadu da aka zuga a wancan lokacin bai kare lafiya ba. Saboda haka shugaban na yanzu yayi hattara kada ya bari fadawansa su zugashi ya bi hanyar Tanja.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG