Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Addinin Musulunci da Na Kirista Sun Yi Taron Neman Zaman Lafiya


Sultan Saad Abubakar Sarkin Musulmi
Sultan Saad Abubakar Sarkin Musulmi

Shugabannin addinan Najeriya a karkashin shugabancin Mai Martaba Sa'ad Abubakar da Cardinal Oaiyekan sun yi taron neman zaman lafiya a arewa da Najeriya gaba daya a Abuja.

Fakewa da addini a kawo asarar jini gurguwar dabara ce da shafa bakin fenti da munafukai keyi shi ne babban jigon taron.

Shugaban darikar Katolika na Sokoto Bishop Matthew Hassan Kukah yana kan gaba a taron. Yace a kowane lokaci babu abun da ake bukata sai dai zaman lafiya domin Najeriya tana cikin matsala. Wannan taron na Musulmi da Kirista sai a natsu a gane cewa ba maganar Musulmi ko Kirista ba ne. Ana maganar rayuwar Najeriya ne.

Shugaban da'awa na Najeriya Dr Aminudeen Abubakar ya gamsu da tasirin taron. Yace da babu dama a taru haka amma sai gashi an taru ba tare da nuna banbanci ba. Taron ya nuna alamun nasara. Kirista yayi kiristanci Musulmi kuma yayi musulunci domin babu tilastawa. Allah Ya ce yana da addininsa su kuma suna da nasu to an samu zaman lafiya.

Amma shugaban kungiyoyin kiristoci reshen arewa maso gabas Rebaran Sha'aibu Tsal yace rashin yin dalla dalla akan jihadi kan kawo dari dari na mabiya. Babban abun dake damun wadanda ba musulmi ba shi ne fasarar jihadi. Sai an sake shiga aji a koyas da mutane. Yace idan da bai zauna da wani musulmi ba wanda ya fasara masa ma'anar jihadi, a da yana ganin ma'anar jahadi ita ce fada da yakar mutane. Ko menene ma ake nufi akwai jahilci a lamarin. Kamar yadda Sarkin Musulmi yace, ta'adanci bashi da fuska.

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya wanke musulunci da zubar da jini ba gaira ba dalili. Har duniya ta tashi Yahudu da Nasara basa yadda sai an bi abun da ransu yake so. Sai dai a yi kokari a fahimci juna. Idan an yi dace ma wani sai ya karbi addinin musulunci.

Akan yawan fada sabili da addini, Kalarawi yace Manzon Allah(S.A.W.) bai yi yakin zubda jini ba. An cuceshi. An koreshi daga garinsa Makka. Bakin ciki yasa ya fita, Sahabansa kuma suka yi kaura zuwa Ethiopia.Bai yi yakin kashe mutane ba amma yakin kare kai yayi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG