Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Shugabannin Afirka Sun Saka Hanu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.


Shugabannin kasashen Afirka a wani taro da suka yi a Addis Ababa na Habasha.
Shugabannin kasashen Afirka a wani taro da suka yi a Addis Ababa na Habasha.
Shugabannin wasu kasashe dake Afirka sun sanya hanu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani aka cimma, da nufin kawo karshen rashin jituwa a gabashin jamhuriyar Demokuradiyyar kwango mai fama da rigingimu.

Yau lahadi ne shugabannin suka sanya hanu kan yarjejeniyar a Addis Ababa na Habasha, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya halarci bikin sanya hanun. Da yake magana, Mr. Ban yace yarjejeniyar “itace matakin farko na wani mashahurin shirin warware rikicin da zai bukaci cigaba da tuntuba”.

Yarjejeniyar tana iya kaiwa ga kafa rundunar hadin guiwa na tsaro a yankin mai abarkatun kasa dake gabashin jamhuriyar demokuradiyyar kwango, domin su tunkari ‘yan tawaye.

Da farko an shirya yin bukin sanya hanu kan yarjejeniyar cikin watan jiya, amma aka dage saboda damuwa da ta taso kan ko wace kasa ce zata jagoranci wannan sabuwar rundunar hadin guiwa idan aka kafa ta.
XS
SM
MD
LG