Janar Abdulsalami Abubakar wanda ya kware a sasanta rikicin siyasa a kasashen Afirka ya yi magana ne a wurin jana'izar tsohon gwamnan jihar Neja Injiniya Abdulkadir Kure.
Inji Janar Abubakar lamarin kasar Gambia nada matukar tayar da hankali. Shawarsa ita ce yadda za'a lallaba Yahya Jammeh ya yadda an kadashi a zaben da ya gabata. Kuma tunda yake yayi mulki har na shekaru 22 yayi hakuri ya sauka domin ba gado ba ne. Ya ba kasarsa lafiya da zama lafiya inji Janar Abubakar.
Yace yadda aka yi zabe da can yaci haka ma aka yi zabe a wannan karon shi Adamu Barrow yaci, saboda haka yayi hakuri ya mika mulki. Ya kira shugabannin kasashen yammacin Afirka da su bi Yahya Jammeh da hankali, bada mugun kalami ba ko wata barazana ba.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.