Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabar Jamus Ce Zakarar Shekara ta 2015


Shugabar Jamus Abgela Merkel
Shugabar Jamus Abgela Merkel

Mujallar Times Magazine ta ayyana shugabar kasar Jamus Angela Merkel a matsayin zakarar shekarar 2015 saboda irin shugabancin da ta nuna wa duniya

Mujallar nan da ake kira Time Magazine, ta ayyana shugabar kasar Jamus Angela Merkel, a zaman "zakarar shekara ta 2015. Mujallar tayi la'akari da shugabancinta a lokacinda ake fuskantar matsalar 'yan gudun hijira daga Syria, matsalar ceto tattalin arzikin Girka, da matsalar kudi da kasashe dake Tarayyar Turai suka fuskanta, da kuma kan katsalandan da Rasha tayi a Ukraine.

Mujallar Time tace, duk lokacinda Turai ta fuskanci matsala ko damuwa nan-da-nan shugaba Merkel zata shigo kuma a sami maslaha.

Editar mujallar Nancy Gibbs, ta rubuta jiya Laraba cewa, ana sanin karfin shugaba, a dai dai lokacinda al'uma suke turjiya, a irin wadanan lokutan ne inji Gibbs, Merkel take shigewa gaba da karfin halin shugabancin da ake karancinsa a duniya baki daya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG