Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabar Koriya Ta Kudu Ta Bayyana Sunayen Wadanda Zasu Maye Gurbin Minitocinta


Shugabar Koriya ta Kudu
Shugabar Koriya ta Kudu

Shugabar kasar Korea ta Kudu Park Geun-hye ta bayyana sunayen wadanda zasu maye gurbim Firaminista da kuma wasu biyu da ga cikin manyan Jami’an gwamnatin kasar a yau Laraba.

Sai dai kuma abokan adawa sun dauki alwashin hana mukaman, inda suka kira nadin a matsayin kokarin janye hankali daga kan binciken hannu dama da tsohuwar kawar shugabar kasar ke dashi acikin binciken wata harkalla da ta taso a kasar.

Park ta tsayar da Kim Byong-Joon, Farfesa a Jami’ar Kookmin a matsayin sabon Firaminista. Mai Magana da yawunta ya kira Kim a mutumin da yayi matukar cancanta da zai iya shawo mafiya yawancin rikita rikitar da kasar ke fuskanta a yanzu, da jogaranci mai karfi domin cigaban Koriya ta Kudu.”

Haka nan Park ta tsayar da Jagoran Harkokin Kudi na Koriya ta Arewa Yim Jong-Yong, a matsayin Ministan Kudi kuma mataimakin Firaminista, san nan Park Seung-joo a matsayin babban Ministan Kula da Jama’a da kuma Tsaro.

Ana ganin wadannan Mukai mai a matsayin kokarin samun dama a wajen ‘Yan adawar Park masu Tsatstsauran ra’ayi. Kim da Park Seun-joo sunyi aiki tare a karshingwamnatin tsohon shugaban karas Koriya ta Kudu Roh Moo-hyu, mai sassaucin ra’ayi.

Amma ‘Yan Adawa sun yi Allah wadai da wannan nadi nan take, inda suka ce anyi shi ne ba tare da tuntubar yan majalisaba sanna suka kira wannan dadi na mamaki da yunkurin kau da kai daga kan Hatsaniyar dake faruwa a yanzu.

Kuri’ar jin ra’ayi nuna goyon bayan yadda da Park da kaso 10, san nan dubunnan mutane sun fita zanga zangaa birnin Seoul a cikin makon da ya wuce don neman Shugabar ta sauka daga kan mukaminta.

XS
SM
MD
LG