Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siriya na bukatar karin tabbaci kafin ta janye dakarunta


Wani babban ramin da tankar yakin dakarun Siriya ta rotsa
Wani babban ramin da tankar yakin dakarun Siriya ta rotsa

Gwamnatin Syria ta ce kafin ta aiwatar da yarjajjeniyar janye

Gwamnatin Syria ta ce kafin ta aiwatar da yarjajjeniyar janye dakarun da Shugaba Bashar al-Assad ya amince da ita, ta na son tartibin tabbaci cewa ‘yan tawaye za su daina fada.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin waje Jihad Makdessi ya fadi yau Lahadi cewa rahotannin da aka yi ta yadawa da farko cewa Syria za ta janye dakarunta daga birane da sauran garuruwa zuwa ran 10 ga wata ba gaskiya ba ne.

Ya ce manzon musamman na MDD da kungiyar kasashen Larabawa Kofi Annan ya kasa gabatar da rubutaccen tabbaci na alkawarin ‘yan ta’adda masu dauke da makamai na daina tashin hankali da kuma shirinsu na ajiye makamai.

Makdissi ya kara da cewa Syria ba za ta yadda a sake maimaita abin da ya faru yayin zuwan masu sa ido na kungiyar kasashen Larabawa cikin Syria a cikin watan Janairu ba, lokacin da y ace dakarun gwamnati sun janye sai kawai su ka ga ‘yan tawaye sun mamaye unguwannin.

A yau Lahadin nan ‘yan rajin kare hakkoki sun ce dakarun Syria sun cigaba da kai hare-hare kan yankunan da ake tawaye a arewaci da kuma tsakiyar kasar, inda su ka kashe tare da raunata mutane da dama.

XS
SM
MD
LG